Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya dace jami'an Amurka su karanta takardar bayani game da batun samar da ayyukan yi a Xinjiang
2020-09-21 20:18:51        cri

A yau Litinin 21 ga wata, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya musunta kalaman wasu jami'an kasar Amurka, dangane da jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake kasar Sin, inda ya yi nuni da cewa, a kwanan baya, ofishin yada labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya kaddamar da takardar bayani kan batun samar da ayyukan yi a jihar Xinjiang. Wadda ta fayyace yadda ake samar da aikin yi a jihar, don haka ya dace a karanta takardar bayanin a tsanake.

Kakakin ya kara da cewa, ana adawa da tilasta wa mutane su yi aiki a jihar ta Xinjiang, tare da kiyaye halastattun hakkokin 'yan kwadago.

Kaza lika kasar Sin ta kalubalanci wasu jami'an Amurka, da su mutunta hakikanin abubuwa, su dakatar da shafa wa Xinjiang kashin kaji bisa hujjar kare hakkin dan Adam, su kuma daina yin shisshigi a harkokin cikin gida na kasar Sin, su sa aya ga illata kwanciyar hankali da wadata a jihar. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakai na wajibi, wajen kiyaye halastattun hakkokin masana'antun kasar Sin. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China