Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar kasar Sin a MDD ta yi watsi da zargin da Amurka ta yiwa kasarta
2020-09-24 12:00:10        cri

Zaunanniyar tawagar kasar Sin a MDD, ta yi watsi da zargi da ma neman bata suna da Amurka ta yiwa kasarta yayin muhawarar babban taron MDD karo na 75 (UNGA) dake ci gaba da gudana.

Tawagar ta ce, Amurkar na kokarin neman bata sunan kasar Sin game da annobar COVID-19, domin dora mata laifi kan gazawarta na dakile cutar. Haka kuma Amurka ta zargi hukumar lafiya ta duniya WHO da ma janyewa daga cikinta, matakin da ya jefa hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da annobar cikin hadari, da cutar da rayukan jama'a a sassan daban-daban na duniya, da ma haddasa dimbin hasara ga 'yan kasarta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China