Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin kasar Sin ya mayar da martani kan zargin da Amurka ta yiwa kasarsa
2020-09-25 10:00:06        cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, jiya Alhamis ya mayar da martani kan zargin da kasar Amurka ta yiwa kasarsa, kan yadda ta tunkari annobar COVID-19.

Kalaman Zhang Jun na zuwa ne, bayan da zaunanniyar wakiliyar Amurka a MDD Kelly Craft, ta sha nanata bukatar da shugaba Donald Trump na Amurkar ya gabatar, na neman dorawa kasar Sin laifin yada kwayar cutar.

Sai dai da yake mayar da martani kan furucin da Kelly Craft ta yi, yayin jawabin da ta gabatar a babban taron muhawarar da aka shirya kan " Tafiyar da harkokin kasa da kasa bayan annobar COVID-19". Zhang, ya bayyana cewa, taron na jiya Alhamis, lokaci ne na sadaukar da kai da yin hadin gwiwa, kamar yadda yawancin mambobin kwamitin sulhun MDD suka bukata. Amma abin takaici a cewar jami'in na kasar Sin shi ne, har yanzu kasar Amurka na furta kalaman da ba su dace da yanayin da ake ciki ba. A don haka, kasar Sin ta nuna adawa da ma watsi da zarge-zarge marasa tushe da Amurkar ke yi mata.

Ya ce, kasar Sin ita ce kasa ta farko da wannan annoba ta harba. Kuma kowa ya ga irin matakan da kasar ta dauka na yaki da wannan annoba. Karkashin jagorancin JKS, al'ummar Sinawa sun hada kansu don yaki da annobar. Managartan matakai da sadaukarwar da kasar Sin ta nuna, gami da gudummawar da ta baiwa kasashen duniya na yaki da wannan annoba, ba boyayyen abu ba ne.

A don haka, ya kamata kasar Amurka ta fahimci cewa, gazawarta na tunkarar annobar, laifinta ne. Idan kuma ana neman wanda za a dorawa wannan laifi, to, babu wanda ya wuce 'yan siyasar kasar.

Zhang Jun, ya ce ya kamata Amurka ta fahimci cewa, zargin wasu kan wannan annoba, ba zai sa ta magance matsalolinta ba. Ko wace kasa tana da nata matsalar da ma hanyar ci gaban ta. A don haka, ya kamata ko wace kasa ta warware matsalolinta ta hanyar da ta dace da ita. Dora laifu kan wasu, ko shirga karya, da zamba, ko sata, babu matsalolin da za su iya warware wa, sai ma kara fadawa hanyar da ba ta dace ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China