![]() |
|
2020-09-23 10:49:13 cri |
Rahotanni daga Najeriya na cewa, jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kubutar da ma'aikatan hukumar kiyaye hadurra ta tarayyar (FRSC) su 26, da wasu 'yan bindiga suka sace a kwanakin baya, a jihar Nasarawa dake tsakiyar kasar.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka shirya a Lafia, fadar mulkin jihar, gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya ce, yana farin cikin sanar da cewa, an saki dukkan ma'aikatan hukumar ta FRSC 26 da 'yan bindiga suka sace a kwanakin baya
Su dai wadannan jami'ai, suna kan hanyarsu ta zuwa wani samun horo ne, a makarantar hukumar ta FRSC dake Udi a jihar Enugu dake kudancin Najeriya, lokacin da wasu da ake zaton 'yan fashi ne, suka yi awon gaba da su.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China