Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Vanguard: Rancen kudin da Sin ta samar wa Nijeriya ya inganta bunkasuwar tattalin arzikinta
2020-08-26 13:18:44        cri

Kwanan baya, jaridar Vanguard ta kasar Nijeriya ta wallafa wani sharhi mai taken "rancen kudi na Sin da 'yancin kasarmu", inda ta bayyana cewa, majalisar dokokin kasar Nijeriya ta zartas da yarjejeniyoyin rancen kudi na kasar Sin, kuma, muradun jarjejeniyoyin sun dace ka'idojin kasa da kasa, rancen kudin da kasar Sin ta samar wa kasar Nijeriya sun taimakawa Nijeriya wajen bunkasu tattalin arziki da raya harkokin zamani, hakika kasar Nijeriya ta karu.

Sharhin ya kuma bayyana cewa, kwanan baya, wasu 'yan Nijeriya sun yi zargin cewa, wasu tanade-tanade dake cikin yarjejeniyoyin rancen kudi sun raunata 'yancin kasar Nijeriya. A hakika, wannan zargi ba shi da tushe, muradin yin watsi da ikon "kiyaye 'yancin kan kasa" da kasar Nijeriya ta ambata alkawari ne na biyan bashinta, bai shafi batun 'yancin kasa ba, kuma bai bata 'yancin kasar Nijeriya ko kadan ba. Kasar Sin ta samar da rancen kudi bisa ka'idojin yarjejeniyar kasuwanci ta kasa da kasa.

Bayanai na nuna cewa, Sin ta samar da rancen kudi na dallar Amurka miliyan 3,121 ga kasar Nijeriya, adadin da ya kai 3.94% na dukkanin bashin kasar Nijeriya, kuma darajin kudin ruwan da za ta biya a ko wace shekara shi ne 2.5%, kuma za a biya bashin ne ciki dogon lokaci.

An yi amfani da dukkanin rancen kudin da kasar Sin ta samar wa kasar Nijeriya wajen samar da ayyukan gina ababen more rayuwa, kamar layin dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna, da layin dogo a cikin birnin Abuja, da layin dogo tsakanin Lagos da Ibadan, da hanyoyin mota na Keffi, da kuma shirin inganta filayen jiragen sama na kasar da dai sauransu, dukkansu sun samar da guraben ayyukan yi a kasar Nijeriya, da ba da muhimmiyar gudummawa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Nijeriya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China