Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tasirin COVID-19 na haifar da barazanar karancin abinci a wasu sassan Najeriya
2020-09-08 20:35:44        cri
Wani rahoton baya bayan nan ya yi nuni da cewa, annobar COVID-19 ta haifar da kamfar abinci a wasu manyan jahohin Nigeria. Alkaluman hukumar kididdigar kasar, sun ce jihohin dake kan gaba wajen fuskantar wannan matsala, sun hada da birnin tarayyar kasar Abuja, da jihohin Kano, da Lagos da Rivers.

Kididdigar ta nuna cewa, kaso 79 na magidantan jihar Rivers, da kaso 72 na magidantan birnin tarayyar kasar Abuja, sun bayyana cewa, su kan tsallake wasu lokutan cin abinci, sakamakon mummunan tasirin da cutar COVID-19 ta yi ga tattalin arzikin su.

To sai dai kuma, tuni babban bankin Najeriyar CBN, ya amince da shigo da tam 262,000 na masara daga waje, domin ragewa 'yan kasar radadin kamfar hatsi da ake fuskanta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China