Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta amince da kudaden shirin kafa sabuwar rundunar 'yan sanda don karfafa tsaro a kasar
2020-08-21 20:55:19        cri
Gwamnatin Najeriya ta amince da samar da naira biliyan 13.3, kwatankwacin dala miliyan 35, kan shirinta na kafa rundunar 'yan sandan al'ummma, a kokarin da kasar ke yi na karfafa amincewa tsakanin 'yan sanda da al'ummomin dake kasar, ta yadda za a magance tashe-tashen hankulan dake faruwa a sassan kasar.

Wata sanarwa da ofishin mataimakin shugaban kasar ya fitar jiya Alhamis, ta bayyana cewa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya amince da samar da kudaden. Burin shugaban dai shi ne sake yiwa harkar tsaron kasar gyaran fuska da ma yadda 'yan sandan za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A jawabinsa, yayin wani taron jama'a kan zaman lafiya da tsaro da aka shirya ranar Laraba a jihar Kebbi dake yankin arewa maso yammacin kasar, babban sifteto janar na 'yan sandan Najeriya, Abubakar Adamu, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayyar kasar ta fahimci muhimmancin hada kai da al'umma, matakin da zai kai ga kafa rundunar 'yan sandan al'umma a kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China