Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa Najeriya yakar COVID-19
2020-08-20 20:34:05        cri
Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya bayyana kudurin kasarsa na ci gaba da baiwa Najeriya taimako da goyon baya a yakin da take yi da cutar numfashi ta COVID-19, har sai ta ga bayan wannan annoba.

Ministan wanda ya bayyana hakan yayin zantawa ta wayar tarho da takwaransa na Najeriya Geoffrey Onyeama, Ya ce, Najeriya babbar kasa ce mai matukar tasiri. Haka kuma kasar Sin tana dora muhimmanci kan matsayin Najeriya da rawar da take takawa a al'amuran duniya, tana kuma dauka tare da raya alakar kasashen biyu daga bangaren tsare-tsare da mahanga na dogon lokaci.

Ya ce, tun lokaci da annobar COVID-19 ta barke, Sin da Najeriya suke taimakawa da goyon baya gami da tsayawa juna. A hannu guda kuma, bangaren kasar Sin ya samarwa Najeriya kayayyakin yaki da wannan annoba da raba fasahohinsa na kandagarkin annobar, baya ga kamfanonin kasar Sin da kungiyoyi da suma suka baiwa Najeriyar taimakon kayayyakin yaki da wannan annoba.

Wang ya jaddada cewa, a halin yanzu yadda ake bincike da samar da rigakafin cutar da ma yadda za a ci gajiyasa, yana ci gaba da janyo hankalin duniya, inda wasu manyan kasashe suke kokarin kwace kasuwar samar da riga kafin tare da mamaye albarkatu, matakin da zai sanya kasashe masu tasowa cikin wani mummunan yanayi

Jami'in na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta sanar da cewa, da zarar ta yi nasarar samar da riga kafin, to za ta samar da shi ga jama'a, don taimakawa kasashe masu tasowa, ciki har da wadanda ke nahiyar Afirka. Ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ingiza wannan shiri da karfafa alakar samar da riga kafi da Afirka.

A nasa bangare, Mr. Onyeama, ya bayyana cewa, Najeriya tana dora muhimmanci kan rawar da kasar Sin take takawa a harkokin kasa da kasa, ta kuma yaba da taimako da goyon bayan da gwamnatin kasar Sin da al'ummar Sinawa ke baiwa Najeriya, abin da ke nuna hadin kai na kut-da kut da 'yan uwantaka dake tsakanin kasashen biyu.

Ya ce, idan ana batun alluran riga kafi, hakika kasashe masu tasowa, ciki har da wadanda ke Afirka, suna cikin matsala. Yana mai cewa, bangaren Najeriya ya yaba matuka da shawarar da kasar Sin ta yanke na mayar da riga kafin a matsayin kayan al'ummar duniya, matakin dake nuna matsayin kasar Sin na babbar kasa da ta damu da halin da duniya ke ciki.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China