![]() |
|
2020-08-22 17:10:27 cri |
A wata sanarwa da aka baiwa kwafenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Juma'a, hukumar sojojin ta ce ta kaddamar da aikin samar da tsaron ne a ranar Lahadi a wasu yankuna dake dajin Dumburum, inda ake zargin barayin suna samun mafaka.
Sojojin sun kashe 'yan bindigar uku a cikin dajin, kana sun kama wasu mutanen 10 da ake zargi a shirin murkushe 'yan bindigar a jahohin Katsina da Zamfara, da sauran yankunan shiyyar arewa maso yammacin kasar, in ji kakakin rundunar sojojin kasar Benard Onyeuko.
A cewar Onyeuko, an gano wasu makamai da harsasai a lokacin samamen, wanda sojojin suka shafe kwanaki suna gudanarwa.
Ya kara da cewa, an yi nasarar kubutar da mutane 10 wadanda 'yan bindigar suka yi garkuwa dasu.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China