Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afirka ta Kudu: Gwamnati za ta mai da hankali wajen raya tattalin arziki
2020-09-09 10:48:15        cri
Jiya Talata, shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa, yanzu, an dawo wasu harkokin tattalin arziki, sakamakon nasarar da aka samu a fannin dakile yaduwar cutar COVID-19 a kasar. Ya ce, a nan gaba kuma, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu za ta mai da hankali kan raya tattalin arziki. Kuma, yana da imanin cewa, bisa kokarin da daukacin al'ummomin kasar suke, tabbas, tattalin arzikin kasar zai karu cikin sauri.

A don haka, ya yi kira ga al'ummomin kasar, da su sauya wannan kalubale zuwa damar neman ci gaba, da kyautata tsohon tsarin gudanarwar da ayyuka, da samar da karin damammaki, ta yadda za a farfado da tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China