Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta Kudu ta sanar da soke zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida don yakar COVID-19
2020-03-25 10:30:13        cri
Kamfanin jiragen saman Afrika ta Kudu na South African Airways (SAA) ya sanar da soke dukkan zirga-zirga ta cikin gida a kasar domin goyon bayan dokar hana fita ta kasar don yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar 27 ga watan Maris zuwa 16 ga watan Afrilu a duk fadin kasar, babban kamfanin sufurin jiragen sama na kasar ne ya sanar da hakan.

Matakin ya biyo bayan umarnin da shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya bayar ne a daren ranar Litinin inda ya sanar da dokar zama a gidaje ta tsawon kwanaki 21 a duk fadin kasar, kuma dokar za ta fara aiki ne daga karfe 12 na daren ranar Alhamis.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China