Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ramaphosa:Wajibi ne gwamnati ta kara karfin rawar da mata ke takawa a harkokin tattalin arziki
2020-08-10 12:14:57        cri
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa, kara shigar da mata cikin harkokin raya tattalin arziki da tabbatar da 'yancinsu a fannin harkokin kudi, zai taimaka wajen magance matsalar cin zarafi da suke fuskanta.

Shugaban ya bayyana haka ne jiya Lahadi, yayin da yake jawabi a bikin ranar mata na wannan shekara ta kafar bidiyo. Yana mai cewa, muddin ana son a kawar da matsalar cin zarafi mai nasaba da jinsi da ma yadda a wasu lokuta mata ke rasa rayukansu, ya kamata gwamnati ta samar da dammakin kasuwanci ga kamfanonin mata.

Ya ce, mataki na farko shi ne, kara samar wa mata damammaki a fannin tattalin arziki, a cewarsa, gwamnati za ta yi haka ne, ta hanyar ware wa harkokin kasuwancin mata kaso 40 cikin 100 na kayayyakin da gwamnatin take saya

Na biyu, a taimakawa matan dake da kamfanoni ko kananan sana'o'I, ciki har da masu zaman kansu. Kuma a halin da ake ciki na nuna daidaito, za a taimakawa kasashe mambobin kungiyar AU, a kokarin da suke yi na rungumar fasahohi na zamani.

A matsayinsa na shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka, Ramaphosa ya bayyana cewa, wajibi ne ragowar gwamnatoci a sassan nahiyar Afirka, su aiwatar da irin wadannan tsare-tsare, ta yadda mata za su dogara da kansu a fannin tattalin arziki. Sai dai a cewarsa, rashin samun jari, na daga cikin abubuwan dake hana matan ci gaba a fannin tattalin arziki.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China