Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun Sin da Afrika ta kudu sun yi muyasar kwarewa kan yaki da COVID-19
2020-04-05 15:59:58        cri

Kwararrun masana kiwon lafiya daga birnin Shanghai na kasar Sin da na kasar Afrika ta kudu sun yi musayar kwarewa game da matakan kandagarki da kuma dakile annobar COVID-19 a lokacin taron tattaunawa da suka shafe sa'o'i biyu da rabi suna gudanarwa ta hanyar bidiyo a daren Juma'a.

Kwararru hudu daga Shanghai, da takwarorinsu sama da goma daga Afrika ta kudu, sun yi musayar ra'ayoyi kan gwaje-gwajen cutar COVID-19, da yadda ake bibbiyar masu dauke da cutar, da yadda ake kula da lafiyar dukkan mutanen da suka yi mu'amala da mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar, sai kuma batun nazari kan samar da alluran rigakafin cutar.

Da yake bayani game da muhimmancin daukar matakan gaggawa wajen tantance masu dauke da cutar, Shen Yinzhong wanda ke aiki a cibiyar kula da lafiyar al'umma ta Shanghai ya ce, kasar Sin ta magance matsaloli ta hanyar tantance marasa lafiyar dake fama da zazzabi a wasu cibiyoyin lafiya da aka kebe domin gudun kada su harbu da cutar a asibitocin da ake jinyar masu dauke da COVID-19.

Zweli Mkhize, ministan lafiyar Afrika ta kudu, ya nuna yabo ga kwararrun masanan hudu daga Shanghai. Ya ce musayar ilmin da kuma kwarewa tana da matukar alfanu kuma suna fatan sake samun makamanciyar wannan dama a nan gaba. (Ahmad Faga)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China