Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Afirka ta kudu za ta sassauta dokar hana fita a watan Mayu
2020-04-24 10:54:41        cri
Shugaban kasar Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa, kasarsa za ta fara sassauta dokar hana fita daga ranar 1 ga watan Mayu mai kamawa, bayan da ya zuwa yanzu, cutar ta halaka mutane 75 a kasar.

Ya ce, gwamnati ta tsara wasu matakan da suka dace, bisa la'akari da yanayin yaduwar cutar a kasar. Yanzu haka dai, kasar tana mataki na biyar na yaduwar cutar, matakin da ke bukatar hana shiga da fita a kasar baki daya, don hana yaduwar annobar.

Daga ranar 1 ga watan Mayu, matakin yaduwar cutar zai yi kasa zuwa mataki na hudu, abin da ke nufin, za a farfado da wasu abubuwa, bisa irin tsauraran matakan da za a dauka.

Shugaba Ramaphosa ya kara da cewa, a lokacin da ake zaman gida karkashin mataki na hudu na yaduwar cutar, za kuma a ci gaba da rufe dukkan iyakokin kasar. Motocin sufurin jama'a za su ci gaba da aiki, ta hanyar daukar tsauraran matakan sanya ido. An kuma haramta tafiye-tafiye tsakanin lardunan kasar, inda ban da safarar kayan abinci da abubuwa masu muhimmanci, kamar yin jana'izar wadanda suka riga mu gidan gaskiya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China