Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Afirka ta kudu za ta tsaurara matakan kandagarkin COVID-19 a wuraren aiki
2020-05-04 09:57:29        cri

Rahotannni daga kasar Afirka ta kudu na cewa, mahukuntan kasar sun sanar da daukar tsauraran matakai don hana yaduwar cutar COVID-19 a wuraren ayyuka, kafin bude wuraren kasuwanci da na dan wani lokaci da ake shirin yi.

Ministan kwadago da ayyukan yi na kasar, Thulas Nxesi shi ne ya bayyana haka, kwana guda kafin sassauta matakan bude wuraren ayyukan yi a yau Litinin, inda ake sa ran mutane miliyan 1 da dubu 500 za su dawo bakin aiki. Bayan da a ranar 1 ga watan Mayu, kasar ta koma mataki na hudu daga mataki na biyar na yanayin yaduwar cutar.

Baya ga matakin bayar da tazara, ministan ya sake sanar da wuraren ayyukan yi, da su rika tantance ma'aikatansu game da alamomin cutar COVID-19 a lokacin da suka dawo bakin aiki, a wani mataki na kare yaduwar cutar.

Ministan ya kuma yi gargadin cewa, duk wuraren aikin da suka gaza daukar matakan da suka dace, hakan na iya zama mummunan laifi da zai kai ga yanke hukunci.

An samu kawuwar wadanda suka kamu da COVID-19 a kasar Afirka ta kudu, tsakanin ma'aikata a wuraren ayyuka. Musamman manyan kantuna na zamani. A Cape Town kadai, an rufe manyan kantunan zamani guda biyar, bayan da aka samu rahoton barkewar cutar a wadannan kantunan a kwanakin da suka gabata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China