Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu karin mutane 82 da suka harbu da COVID-19 a Afirka ta kudu
2020-04-03 11:02:34        cri
Ministan lafiya a Afirka ta kudu Zweli Mkhize, ya ce an samu karin mutane 82 da suka harbu da cutar numfashi ta COVID-19 a jiya Alhamis. Ya zuwa yanzu dai jimillar wadanda ke dauke da cutar a kasar ya kai 1,462, kuma tuni cutar ta hallaka mutane 5.

Akwai kuma sanannen masanin cutar HIV dan kasar wato Gita Ramjee, wanda ya rasu a ranar Talata a Dubai, sakamakon harbuwa da cutar ta COVID-19. An ce Mr. Ramjee mai shekaru 64 a duniya, ya harbu da cutar ne yayin wani balaguron da ya yi a kwanan baya zuwa London.

To sai dai ministan lafiyar ya ce ba a samu karuwar wadanda cutar ta hallaka ba tun daga ranar Laraba. Mr. Zweli Mkhize ya bayyana hakan ne a Bloemfontein na lardin Free State, lokacin da ya ziyarci asibitin kwararru na Universitas Academic.

Mr. Mkhize ya kuma yi kira ga al'ummar Afirka ta kudu, da su rungumi shawarar zama a gida da gwamnati ta ayyana, tun daga tsakar daren ranar 26 ga watan Maris, a wani mataki na dakile yaduwar cutar. Rahotanni na cewa, ana samun yawaitar masu karya wannan doka a sassan kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China