Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba wanda zai hana farfadowar kasar Sin
2020-09-04 15:27:28        cri

Da yammacin jiya Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi jawabi yayin taron karawa juna sani game da cikar shekaru 75, tun bayan da al'ummun Sinawa suka yi nasarar yakin kin jinin harin Japanawa, kuma shekarar cika shekaru 75 da al'ummun kasa da kasa suka yi nasarar yakin kin tafarkin murdiya.

Cikin jawabinsa, Xi Jinping ya bayyana muhimmiyar ma'anar cimma nasarar wannan yaki, ya kuma ce, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan fannoni guda biyar, domin samun farfadowar kasar Sin baki daya.

Cikin wadannan shekaru 75 da suka gabata, kasar Sin ta samu babban sauyi, ta kuma cimma nasarori da dama. A nan gaba kuma, shugaba Xi ya ce, "Za mu tsaya tsayin daka a fannoni biyar, wato bin jagorancin JKS, da bin tsarin gurguzu na musamman na kasar Sin, da mai da bukatun jama'a a gaban komai, da ci gaba da dukufa, da kuma neman bunkasuwa ta hanyar zaman lafiya." Kuma wadannan su ne dalilan da suka sa kasar Sin, ta sami babbar bunkasuwa, sun kuma nuna ra'ayin shugaban kasar Sin kan yanayin da muke ciki.

Haka kuma, "neman ci gaba cikin zaman lafiya" shi ne alkawarin da kasar Sin ta yi wa gamayyar kasa da kasa, amma, wasu 'yan siyasan kasar Amurka su kan bata sunan kasar Sin, domin kiyayyarsu ga kasar, lamarin da ya kawo barazana ga zaman lafiyar kasa da kasa. Shi ya sa, cikin jawabinsa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, "Dukkanin al'ummomin kasar Sin ba za su yarda da hakan ba". Hakan dai ya nuna matsayin kasar Sin na bin ka'idojinta na neman ci gaba ta hanyar zaman lafiya.

Har ila yau, shugaba Xi ya sake yin gargadi ga wadanda suke neman bata yunkurin kasar Sin na neman farfadowa, ya ce al'ummomin kasar Sin ba sa tsoronsu, domin babu wanda zai iya hana al'ummomin kasar neman farfadowar kasarsu bai daya.

Jawabin da shugaba Xi ya yi ya samu amincewar gamayyar kasa da kasa. Wasu ma sun ce akwai wuya, a kai ga kafa tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu, kuma ya kamata a yi koyi daga darussan tarihi, da hada kai wajen shimfida zaman lafiya tsakanin kasa da kasa, da neman ci gaba cikin lumana.

Game da hakan, ministar harkokin watsa labarai ta kasar Zimbabwe Monica Mutsvangwa, ta bayyana cewa, dabarar kasar Sin ta samun gagarumin ci gaba, ita ce girmama 'yancin kai na ko wace kasa, wadda ta kasance abin koyi ga kasa da kasa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China