Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yaki da talauci: Kasar Sin ta yi farar dabara kan matakan yaki da talauci
2020-08-31 17:19:28        cri

Masu hikimar magana na cewa dabara ba ta daure kaya dole sai an hada da igiya, kuma a shuka alheri don wata rana za a girba. Tun bayan da jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin ta aiwatar da manufarta na gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, ta kaddamar da muhimman kudurorin gina kasa da raya cigaban al'ummarta. Batun yaki da fatara wani muhimmin jigo ne daga cikin muhimman ajandodin bunkasa ci gaban kasar Sin. Domin sai da ruwan ciki ake jan na rijiya. Wannan ne dalilin da ya sa mahukunta kasar Sin suka dukufa tare da maida hankali wajen ganin an aiwatar da shirin yaki da fatara yadda ya kamata domin taimakawa al'ummomin kasar masu fama da talauci don su samu zaman wadata da walwala da kuma samun farin ciki a rayuwarsu ta yau da kullum. Shekarar 2020, ta kasance shekarar da gwamnatin Sin ta ayyana ta a hukumance a matsayin shekarar cimma nasarar kammala tsame jama'ar kasar daga kangin talauci, gami da samar da yanayin zaman rayuwar al'ummar Sinawa mai matsakaiciyar wadata, ko da yake, annobar cutar shekewar numfashi ta COVID-19 ta haifawar duniya cikas ta fuskar aiwatar da manufofi a kasashen duniya daban daban. Amma duk da haka, mahukuntan kasar Sin suna ci gaba da yin iyakar bakin kokarinsu domin ganin an cimma nasarori kan manufofin da aka sanya a gaba musamman kan wannan muhimmin shiri na yaki da kangin fatara.

A kwanakin baya ofishin kula da shirin yaki da talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da sanarwa, inda ya nuna cewa, kawo yanzu, adadin cinikin da aka samu na kayayyakin da aka samar karkashin shirin yaki da fatara ya zarce yuan biliyan 100 a wannan shekara ta 2020.

A cewar Wang Dayang, mataimakin daraktan sashen hukumar yaki da fatara na ofishin majalisar gudanarwar kasar, ya bayyana cewa bangarorin da abin ya shafa suna tallata kayayyakin da ake samarwa karkashin shirin yaki da fatara ta hanyar kafa sassan dake yin kasafi domin sayen kayayyakin da aka samar da kuma sayar a kasuwanni karkashin shirin yaki da fatarar da gwamnatin Sin ta bullo da shi, wanda ya hada da zaburar da kamfanoni da kungiyoyin al'umma da su tallata kayayyakin da ake samarwa.

A wata kididdigar baya bayan nan da sashen kula da shirin yaki da fatara na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar ya nuna cewa, ya zuwa yanzu, an samar da jimillar kayayyaki karkashin shirin yaki da fatara 76,152 a larduna 22 dake tsakiya da yammacin kasar Sin, kuma baki daya sun yi cinikin sama da Yuan biliyan 102.7. Hakika wannan babbar nasara ce, kuma za mu iya cewa lallai gwamnatin Sin ta yi farar dabara a karkashin shirinta na yaki da talauci da kuma aniyarta na samar da zaman wadata da walwala a tsakanin al'ummar Sinawa. Tabbas, yabon gwaji ya zama tilas. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China