Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Me ya sa kasuwar fina-finai ta kasar Sin ta farfado da sauri
2020-08-28 16:03:13        cri

Idan ana maganar fina-finai a halin yanzu, to ba zai wuce wani fim mai suna The Eight Hundred wanda aka kaddamar a ranar 21 ga wata a gidajen sinima dake fadin kasar ba, wanda a cikin mako guda aka sayi tikitin kallon fim din da ya kai sama da Yuan biliyan 1.4, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 200. A wani gidan sinima da ke birnin Chengdu, hedkwatar lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, jama'a sun shiga dogon layi don kallon fim din, kowa na cikin murnar samun damar kallon fim a cikin gidan sinima bayan da gidajen sinima suka shafe sama da rabin shekara a rufe.

A hakika, an kaddamar da fim din ne a daidai lokacin cikar wata guda da sake bude gidajen sinima a kasar Sin. Alkaluman kididdiga na nuna cewa, ya zuwa ranar 20 ga wata, yawan kudin tikitin kallon fina-finai da aka sayar a gidajen sinima na fadin kasar ya zarce yuan biliyan guda, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 140, kuma kaso 83% na gidajen sinima na kasar sun koma bakin aiki, wadanda kuma suka karbi masu kallo kimanin miliyan 33, alkaluman da suka shaida yadda harkokin fina-finai ke saurin farfadowa fiye da yadda aka yi hasashe. Haka kuma fim din mai taken The Eight Hundred ya kara karfafa gwiwar jama'a dangane da farfadowar kasuwar fina-finai a kasar.

Kasuwar fina-finai ta kasar Sin ta farfado ne a sakamakon yadda aka shawo kan cutar Covid-19 yadda ya kamata. Barkewar annobar Covid-19 a farkon shekarar da muke ciki, ya haifar da babban kalubale ga bunkasuwar harkokin fina-finai, kuma a nan kasar Sin, an rufe gidajen sinima a fadin kasar don dakile yaduwar cutar. A sakamakon kwararan matakan da kasar Sin ta dauka, an samu nasarar shawo kan annobar, har ma a ranar 20 ga watan Yulin da ya gabata, an fara bude gidajen sinima a sassan da ba sa fuskantar barazanar annobar a fadin kasar, tare da daukar matakai na kandagarkin cutar, ciki har da kayyade yawan masu kallo da bukatar masu kallo su sanya marufin baki da hanci a lokacin kallon fim, da kuma kiyaye tazarar da ta wajaba a tsakanin su da sauransu.

Farfadowar kasuwar fina-finai ta kasar Sin ta kuma jawo hankalin kafofin yada labarai na Amurka, inda kafar yada labarai ta CNBC ta kasar ta wallafa wani bayanin cewa, dalilin da ya sa Amurka ba ta kai kasar Sin saurin farfadowar kasuwar fina-finai ba shi ne, sabo da kasar Sin ta dauki managartan matakai har ta shawo kan annobar, a yayin da Amurka ta boye yanayin annobar. Ta kuma kara da cewa, saurin farfadowar kasuwar fina-finai wata kyakkyawar alama ce ga kasashen duniya.

Ban da kasuwar fina-finai, tattalin arzikin kasar Sin ma ya amfana da matakan da kasar ta dauka na kandagarkin cutar. A wani bayanin da jaridar Wallstreet Journal ta wallafa a kwanan baya, ta ce, tattalin arzikin kasar Sin na farfadowa cikin sauri. Ta ce, duk da cewa akwai kalubale da kasar ke fuskanta, amma al'ummar kasar na jin dadin rayuwarsu fiye da akasarin takwarorinsu na kasashen yammaci a sakamakon farfadowar tattalin arzikin kasar. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China