Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me Ya Sa Mike Pompeo Da Ba Shi Da Wata Kima Ba Ya Jin Kunya?
2020-09-01 21:27:01        cri

Kwanan baya, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya yi shela a shafin sada zumunta ta yanar gizo cewa, kasar Sin ta raya tattalin arzikinta ba tare da kare muhalli ba. Dangane da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kamata ya yi Mr. Pompeo ya kalli kansa sosai.

Sanin kowa ne cewa, 'yan siyasan Amurka sun janye Amurka daga yarjejeniyar Paris bisa son rai, lamarin da ya kawo cikas wajen rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli a duniya. Tuni dai kimar 'yan siyasan Amurka ta zube a idon duniya. Me ya sa Pompeo ba ya jin kunya, yana ta sukar sauran kasashe game da batun kiyaye muhalli?

Raya tattalin arzikin kasar ba tare da gurbata muhalli ba, halin musamman ne da kasar Sin take da shi wajen raya kasa. A shekarun baya, kasar Sin ta rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, yayin da muhallin halittu yake samun kyautatuwa sosai. Har ila yau kasar Sin ta aiwatar da yarjejeniyoyin kasa da kasa da ta kulla yadda ya kamata. Haka kuma tana kara zuba jari a fannin makamashin da ake iya sabuntawa a duniya. Tana kuma ba da gudummowa wajen kyautata muhallin duniya. Amma Pompeo bai lura da wannan ba. Yana ta neman shafa wa kasar Sin wadda ke kokarin raya kanta ba tare da gurbata muhalli ba kashin kaji. Sakamakon abubuwan da yake yi, ya sa dukkan kimar Amurka ta zube a duniya.

Ban da batun kiyaye muhalli, gwamnatin Amurka mai ci ta sha janyewa daga yarjejeniyoyin kasa da kasa, tare da ci gaba da cin zalin wasu kasashe. Amma abun da ya ba mutane dariya shi ne, Mr. Pompeo da sauran irinsa suna ci gaba da kiran kansu "kakakin gamayyar kasashen duniya", suna ci gaba da yin wasan yara ta fuskar siyasa. Mr. Pompeo mai son kai idan ya ci gaba da yin haka, to, zai zama babban maras kunya a tarihi. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China