Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kada Wasu 'Yan Siyasan Amurka Su Ci Amanar Tarihi
2020-09-02 20:59:37        cri
Gobe Alhamis 3 ga watan Satumba, shekaru 75 ke nan da samun nasarar yaki da mahara Japanawa a kasar Sin da kuma nasarar yaki da 'yan Nazi a duniya baki daya. Al'ummar Sin sun shafe shekaru 14 suna sadaukatar da rayukan mutane miliyan 35, daga karshe, sun samu nasarar korar mahara Japanawa daga kasar ta Sin. Sun kuma ba da babbar gudummawa wajen samun nasarar yaki da 'yan Nazi a duniya. Idan aka kalli tarihi, to, za a kara fahimtar manufar da za a bi a nan gaba. Duk wadanda suka jure wahalar yake-yake ba su son maimaita abubuwan da suka wakana a baya. Yanzu haka kasashen duniya suna kokarin samun zaman lafiya da bunkasuwa.

Amma abin da ba yake addabar mutane shi ne, yayin da barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta kawo illa ga tsarin siyasa da tattalin arzikin duniya, wasu 'yan siyasan kasar Amurka ba su tafe daidai da zamani ba, sun yi ta shelar tayar da sabon yakin cacar baki, sun kuma rura wutar nuna kiyayya ga juna.

A halin yanzu ana fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsa a baya ba a duniya. Kasashen Sin da Amurka suna da sabani a tsakaninsu a fannonin ko za a bi manufar cudanyar sassa daban daban ko kuma ra'ayi na kashin kai, ko za a nemi yin hadin gwiwar moriyar juna ko kuma cin moriyar wani kuma ya yi hasara. 'Yan siyasan Amurka da dama sun fi fifita muraddunsu fiye da muraddun sauran kasashen duniya. Sun rura wutar nuna kiyayya da ma yin adawa da juna, suna fatan rashin samun zaman lafiya a duniya. Sun manta da abubuwan da suka faru a tarihi, sun nemi a sake tafka kuskuren da aka yi a baya. Idan har haka ya faru, a hakika dai tarihi ba zai yafe su ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China