Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan Siyasan Amurka Sun Yi Karya Kan Jihar Xinjiang
2020-09-03 21:18:07        cri

Ranar 3 ga wata, cibiyar nazarin bunkasar jihar Xinjiang ta kasar Sin ta kaddamar da wani rahoto, inda aka yi karin bayani kan batun yawan al'ummar jihar ta Xinjiang, inda rahoton ya musunta karya mai ban tsoro da wasu 'yan siyasan Amurka suka yi dangane da yawan al'ummar jihar da batutuwn da suka shafi haihuwa bisa ga alkaluma filla-filla da hakikanin shaidu. Wasu gamsassun shaidu sun tono ainihin makarkashiyar wasu 'yan siyasan Amurka ta illanta kwanciyar hankali da wadata a jihar Xinjiang da sunan "kiyaye hakkin dan Adam", da kuma neman cimma muradunsu na siyasa.

Sanin kowa na cewa, batun Xinjiang, batu ne da ke shafar yaki da 'yan ta'adda, da yin adawa da kawo baraka ga kasar Sin. A don haka, bai shafi hakkin dan Adam, ko al'umma, ko addini ba. Sakamakon jerin matakan da gwamnatin kasar Sin take dauka domin yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi a jihar, ya sa aka samu kwanciyar hankali da wadata a wurin. Al'ummomin Xinjiang sun ci gajiyar bunkasar jihar sosai, inda kuma ake kyautata ba da tabbacin zaman al'ummar kasa, da kare dukkan hakkokin al'ummomin jihar.

A daren ranar 1 ga wata ne jihar ta Xinjiang ta samu farfadowa daga dukkan fannoni yayin da take ci gaba da dakile da kandagarkin cutar COVID-19. Kafofin yada labaru na wurin sun ruwaito cewa, yanzu haka, rukunin farko na masu yawon shakatawa suna kan hanyar zuwa jihar. Kasar Sin tana maraba da dukkan mutanen da suke kula da jihar Xinjiang da su ziyarci jihar. Tabbs karyar da aka yi kan batun Xinjiang da kuma bata sunan kasar Sin ba za su yi nasara ba, saboda shaidun dake bayyane a zahiri. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China