Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yakin kin jinin harin Japanawa ya haskawa duniya muhimmancin zaman lafiya da hadin kan kasa da kasa
2020-09-03 19:05:17        cri

Kasancewar bana ake cika shekar 75 tun bayan da al'ummun Sinawa suka yi nasarar yakar harin Japanawa, kuma shekara ta cikon 75, bayan da al'ummun kasa da kasa suka yi nasarar yakar tafarkin murdiya, masharhanta da dama ke ta tofa albarkacin bakinsu, game da irin darussan da yake-yake suka koyar ga daukacin bil Adama, ko hakan ya zamo wata dama, ta kara darajta zaman lafiya da daukacin al'ummun duniya ke fatan dorewarsa.

Masana tarihi, da masu fashin baki daga sassan duniya daban daban, sun yi amanar cewa, yakin kin jinin harin sojojin Japanawa da al'ummun Sinawa suka yi, ya taka babbar rawa wajen cimma nasarar yakar tafarkin masu mulkin danniya, wato Fascism, wanda al'ummun kasashen duniya suka yi farin ciki da shi.

Kamar dai yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, cewar albarkacin ranar tunawa da wannan yaki na kin harin sojojin Japanawa, mummuman sakamakon yakin ya kara sanya al'ummun duniya darajta zaman lafiya. Kaza lika yakin ya tunawa duniya kimar sadaukarwar da Sinawa 'yan mazan jiya suka yi, wajen sadaukar da rayuwarsu, domin zuri'ar su ta gaba ta ci gaba da wanzuwa cikin salama.

Duk da kasancewar yake-yake da suka gabata, sun kasance madubi dake nusar da bil Adama kimar zaman lafiya, a hannu guda kuma, halin da duniya take ciki a yanzu ma yana tattare da yanayi na rashin tabbas. Zama lafiya da ci gaba na fuskantar barazana, daga masu yunkurin farfado da yakin cacar baka, da masu kokarin bin ra'ayin kashin kai, da masu watsi da cudanyar sassa daban daban. Duniya na fuskantar kalubalen kariyar cinikayya, da nuna kyamar wasu al'ummu, ko nuna wariyar launin fata. Dukkanin wadannan alamu ne dake nuna cewa, har yanzu akwai sauran rina a kaba.

Ko shakka babu, kamata ya yi sassan kasa da kasa su nacewa darussan tarihi, su kara azama wajen wanzar da zaman lafiya, da manufofin gina duniya mai kyakkyawar makoma ga dukkanin bil Adama.

Idan kuma har ana son zaman lafiya ya dore, ya zama wajibi a samar da al'ummar duniya mai hadin kai. A kaucewa nunawa juna kiyayya, da kyama, da banbanci, duba da cewa, wadannan akidu ne ke kaiwa ga yake-yake, wanda kan haifar da masifu da kunci ga duniya baki daya.

A gabar da ake tunawa da wadannan shekaru na karshen yake-yake, musamman ma yakin kin jinin harin Japanawa, da kuma na adawa da masu bin tafarkin murdiya, ya dace duniya ta rungumi akidun mutunta juna, da wanzar da daidaito, da habaka zaman lafiya da ci gaba, da cimma manufa guda ta dora duniya kan turba mai bullewa, wadda kowa zai amfana da ita.

Fatan dukkanin masu kaunar zaman lafiya shi ne, dukkanin sassan kasa da kasa za su hada karfi da karfe, wajen goyon bayan ka'idojin cudanyar kasa da kasa cikin lumana, karkashin inuwar hukumomi kamar MDD da sauran su, matakin da ko shakka babu, zai haifar da dama ta cin moriyar juna, da fadada nasarorin wanzar da zaman lafiya mai dorewa, da kyakkyawar rayuwa ga dukkanin al'ummar duniya. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China