Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Chongqing Ya Samar Da Guraben Ayyukan Yi Ta Hanyar Watsa Shirin Bidiyo Kai Tsaye
2020-08-30 21:24:36        cri
Sakamakon barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, ya sa da wuya ne ake iya daukar ma'aikata a zahiri, don haka mahukuntan birnin Chongqing dake yankin tsakiya maso yammacin kasar Sin sun gaggauta kara bada hidima ta kafar yanar gizo, sun kafa wani dandalin daukar ma'aikata ta hanyar watsa shirin bidiyo kai tsaye cikin himma da kwazo, inda aka gwada kamfanoni a zahiri da kuma daukar ma'aikata ta hanyar watsa shirin bidiyo kai tsaye. Mahukuntan birnin sun kirkiro wata sabuwar hanyar daukar ma'aikata da samun guraben ayyukan yi ta kafar yanar gizo.

Tun daga ranar 20 ga watan Yunin bana har zuwa yanzu, a kowace ranar Jumma'a da karfe 3 na yamma, ana daukar ma'aikata ta hanyar watsa shirin bidiyo kai tsaye a birnin na Chongqing, inda aka gwada kamfanoni a zahiri cikin hoton bidiyo, ma'aikatan kamfanonin sun bayyana ra'ayinsu kan yadda suke gudanar da aiki, sa'an nan, an yi karin bayani kan albashin da za a bayar. Sassa daban daban na mahukuntan Chongqing sun kafa wannan dandali ne cikin hadin gwiwa.

Alkaluma sun nuna cewa, shirye-shiryen bidiyo guda 8 na farko da aka watsa kai tsaye sun jawo 'yan kallon miliyan 1 da dubu 648 baki daya, haka kuma, kamfanoni dubu 11 da dari 6 sun samar da guraben ayyukan yi dubu 124 da dari 6, sun kuma karbi takaitaccen tarihin masu neman aikin yi guda dubu 305, mutane 9678 sun samu aikin yi.

Yanzu haka kamfanoni da dama a Chongqing suna daukar ma'aikata ta kafar yanar gizo. Li Weimin, shugaban hukumar kula da hidimar samun aikin yi ta birnin ya yi bayani cewa, nan gaba za a dauki ma'aikata ta hanyar watsa shirin bidiyo kai tsaye a kullum, sa'an nan za a watsa bidiyon musamman kai tsaye tsakanin wadanda suka gama karatu daga jami'a, da kuma kamfanoni mallakar gwamnati, a kokarin kara samar da ayyukan yi. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China