Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kawar Da Talauci Ta Hanyar Raya Sha'Anin Yawan Shakatawa A Kauyen Lardin Shanxi
2020-08-03 16:23:13        cri

Kauyen Songjiagou na gundumar Kelan ta lardin Shanxi ya zama muhimmin kauye mai raya sha'anin yawon shakatawa karo na farko a nan kasar Sin a shekarar bara, wurin da ya ja hankalin masu yawon shakatawa masu dimbin yawa daga gida da waje.

Shekaru 2 da suka gabata, kauyen Songjiagou na matsayin wani matsungunin da aka kafawa mutanen da suka kaura daga wasu wurare don kawar da kangin talauci, mutane 265 daga kauyuka 14 da suke kewaye shi sun kaura zuwa wannan kauye, dukkansu mutane ne da suka yi fama da talauci mai tsanani.

Bisa raya sha'anin yawon shakatawa tare da mai da hankali kan aikin gona, duk mazauna kauyen Songjiagou sun fito daga kangin talauci daga shekarar 2017, ya zuwa karshen shekarar 2018, yawan kudin shiga na ko wane mutum ya kai yuan 8816.

Gagarumin sauyin da kauyen ya samu, ya ja hankalin matasa da dama da suka koma garinsu don kafa harkokinsu.

Gwamnan gundumar Hou Junsheng ya ce, aikin dake gaba shi ne tabbatar da ba a koma cikin talauci ba, da daukar matakan da suka dace don kara kudin shigar manoman wurin, ta yadda za su iya samun wadata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China