Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Al'ummar kabilar Zang sun fita daga talauci bisa manufofin gwamnatin kasar Sin
2020-07-31 13:56:22        cri

Chendrup Dekyi mai shekaru 50 da haifuwa, ita ce mai dakin kwana da ake kira "gidan Chendrup Dekyi". A cikin gidanta, akwai wani zane dake jawo hankalin mutane sosai, inda aka zana wasu gidaje da dama dake kan tsaunuka, kana galibin gidajen sun yi kama da wata fadar gargajiya mai salo irin na Turai. A cikin shekaru 14 da suka gabata, Chendrup Dekyi ta dogara da wannan fadar wajen fitar da kanta daga talauci, tare da samun rayuwa mai wadata. Kudin shigar da ta samu a shekarar 2017, bisa otel da ta mallaka, ya kai kudin Sin RMB dubu 140. A bara an rufe otel har tsawon watanni uku, don a yi masa gyaran fuska, duk da hakan kudin shigar da ta samu a shekarar ya kai dubu 70.

Wannan zanen dake cikin gidanta ya nuna mana tsarin wata fadar gargajiya ta daular Gurge ta kabilar Zang dake gundumar Zanda na yankin Ngari, ta kan kuma jawo hankalin masu bude ido na gida da waje matuka a ko wace shekara. A gindin wannan tsauni akwai wani kauye, inda Chendrup Dekyi ke zama a ciki. A shekarar 2006, mazauna kauye sun fara karbar baki 'yan yawon bude ido a cikin gidajensu. A shekarar 2019, iyalai 32 masu gadaje 480 sun karbi masu yawon shakatawa kimanin dubu 18, inda yawan kudin da suka samu ya kai fiye da RMB Yuan miliyan 1.62.

A karkashin manufar gwamnatin kasar Sin na baiwa jihar Tibet taimako don kawar da kangin talauci, wannan kauye ya samu taimako daga birnin Shijiazhuang na lardin Hebei a 'yan shekarun baya-baya , inda aka gina sabbin gine-gine 36, wadanda fadinsu ya kai kimanin muraba'in mita 6100, kana yawan kudin da aka zuba ya kai Yuan miliyan 25. Matakin da ya amfani mutane 144 a magidanta 36 a kauyen. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China