Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kawar da talauci a tudu mai tsayi a kasar Sin
2020-07-27 15:19:41        cri

Yang Maolu, dan birnin Yulin na lardin Shaanxi na kasar Sin mai shekaru 61 ne a duniya, yana noman ganyayen lambu da kankana a yankin Ngari na jihar Tibet har shekaru 11. Lokacin da ya yi zama a Yulin, ya taba noma wani kabewa mai nauyi fiye da 55kg, wanda aka saye shi da kudi RMB 5000.

A cikin lambun gona na gundumar Gar na yankin Ngari, ya shawarci shugabansa noman kabewa, don kabewa na da kyaun gani. Yankin Ngari na kan tudu mai tsayi fiye da mita 4500, babu tsuntsu da su iya ratsa wannan wuri balle aka shuka ciyawa, amma Yang Maolu ya yi iyakacin kokari yana noman kabewa a wannan wuri mai tsayi fiye da mita 4500, har wani da ya shuka a bara ya kai fiye da kilo 70, wani daban da ya shuka a bana ya kai kilo 100.

Yang ya ce, ya fara noman kayayyakin lambu ne tun lokacin da yake da shekaru 30 da haifuwa, bayan ya zo nan, abokan kabilar Zang da kuma shugabanni suna maraba da shi matuka, yana zaman rayuwa cikin nishadi sosai.

Gundumar Gar tana makwabcin yankin Kashmir mai mallakar Indiya, wadda ta kasance daya daga cikin gundomomi 21 dake kan iyakar kasa a yankin Tibet, matsakaicin tsayinta ya kai fiye da mita 4500, yawan mazauna ya kai dubu 42, kabilu 27 suna rayuwa a nan ciki hadda kabilun Zang da Han.

Gwamnatin gundumar ta fara tattara kudin kafa lambun noma a wurin daga shekarar 2011, domin samar da isasshen kayayyakin ganyaye da kara samar da guraben aikin yi da kawar da kangin talauci. Ya zuwa yanzu, an zuba kudi da ya zarce miliyan 60 don kafa wannan lambun noma na zamani mai fadi fiye da hekta 53 dake da akwatuna kiyaye zafi 161 da kuma gidajen noman kankana 66. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China