Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kawar da kangin talauci ta hanyar ba da ilmi a yankin Liangshan ta kabilar Yi mai cin gashin kanta na kasar Sin
2020-07-22 16:29:15        cri

Yankin Liangshan ta kabilar Yi mai cin gashin kanta na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, wuri ne mafi girma da al'ummar kabilar Yi suke rayuwa.

Shekaru biyu da suka gabata, shugaba Xi Jinping ya ziyarci gidajen matalauta dake kauyen Sanhe dake cikin tsaunin Da Liangshan mai zurfi, inda ya nuna cewa, kaurar da matalauta zuwa sabbin gidaje hanya ce mai amfani wajen tallafa musu, kuma kamata ya yi a tabbatar da wannan aiki. A cikin wadannan shekaru biyu, kauyen Sanhe ya kafa matsugunai 9 don kaurar da matalauta, inda matalauta iyalai 147 mai kunshe da mutane 801 suka kaura zuwa sabbin gidaje. Wani dan kauyen ya ce, kamata ya yi mazaunan wurin su yi kokarin fita daga kangin talauci da samun zaman rayuwa mai wadata, ganin taimako mai kyau da gwamnatin ke ba su.

Yayin da shugaba Xi ya ziyarci yankin tsaunin Daliangshan, ya ce, kamata ya yi a mai da hankali kan aikin ba da ilmi don kada a bar yara cikin jahilci, wanda abu ne dake haifar da talauci. Ya zuwa yanzu, yawan yaran dake kasa da shekaru 7 da suka shiga makaranta ya karu zuwa 84.03% idan aka kwatanta da 55.4% na shekarar 2015, makarantun kananan yara a kauyen ya kai fiye da 3000. 'Yan kauyen sun ce, wadannan makarantu iri daban-daban na samar da haske mai kyau ga makomar al'ummar Daliangshan. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China