Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sha'anin shuka inabi ya taimaka wajen kawar da talauci a lardin Sichuan na kasar Sin
2020-07-24 14:15:15        cri

A shekarun nan na baya-baya, kauyen Guoyuan na birnin Meishan na lardin Sichuan na kasar Sin ya raya aikin musamman bisa dogaro da halin da yake ciki da fasahar zamani, inda ake kokarin kawar da talauci ta hanyar shuka inabi, har yawan kudin da aka samu daga wannan aiki ya kai fiye da kudin Sin RMB yuan miliyoyi, matakin da ya baiwa mazaunan wuri zaman rayuwa mai nishadi.

Manomi Zhang Xiong yana farin ciki sosai, saboda bai jima da kulla kwangila da wani kamfani ba, ya ce, ana bukatar inabin wurin sosai, kuma kamfanoni da dama sun sa hannu kan yarjejeniya da su tun kafin inabin su nuna.

Kafin a fara wannan sha'ani a wurin, Zhang Xiong ya yi gwagwarmaya don neman kudin shiga, a wancan lokaci manoma su kan gudanar da ayyuka bisa salo irin na da, abun da ya dogara da yanayi matuka.

Sakataren JKS na kauyen Li Yongwei ya ce, kauyen ya gayyaci masana daga jami'ar Sichuan don su yi nazari, su samarwa kauyen wata dabarar raya noman inabi ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani.

Ban da wannan kuma, kauyen ya tamakawa 'yan kauye ciki hadda Zhang Xiong don su samun rancen kudi. Kazalika, kauyen ya ba da tallafi wajen gyara hanyoyi da ingancin filaye da shigo da irrai masu inganci.

Har ila yau, dukkannin manoman kauyen Guoyuan sun fito daga kangin talauci, yawan kudin shiga na kowane mutum ya kai yuan dubu 31 a ko wace shekara bisa dogaro da wannan sha'ani, wanda ya ninka sau 15 bisa na lokacin baya wato kafin suka fara shuka inabi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China