Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kafa tashoshin kula da yanayi masu sarrafa kansu a kauyuka da garuruwan kasar don yaki da talauci da riga kafin aukuwar balai
2020-08-10 11:01:00        cri

Kasar Sin ta yi nasarar kammala aikin kafa tashohin kula da harkokin yanayi masu sarrafa kansu guda 1185 a kauyuka da garuruwan kasar masu fama da talauci kamar yadda aka tsara, biyo bayan turawa muhimman bayanai dake cikin irin wadannan sabbin na'urorin kula da yanayi 448 da aka girke a lardin Sichuan.

Kammala wannan aiki ya kawo karshen matsalolin karancin tashoshin kula da yanayi masu sarrafa kansu da aka dade ana fuskanta, da bayanan yanayi game da yankuna da a baya ba a samu, da rashin karfin yankunan kasar masu fama da talauci game da sanya ido kan aukuwar bala'u.

A yayin da ake kokarin gina tashoshin kula da yanayi masu sarrafa kansu da nufin kawar da talauci, sassan kula da yanayi da takwarorinsu dake matakai na kauyuka kan yaki da talauci, sun kafa tashoshin tallafawa jama'a wajen sanya ido kan yanayi a kokarin da ake na yaki da talauci, don samar da taimakon da ya dace ga matalauta.

Yanzu haka, sassan kula da yanayi a larduna 8 da suka hada da Tibet da Mongolia ta gida da Sichuan, sun kafa tashoshin tallafawa jama'a game da sanya ido kan yanayi, wadanda suka ba da gagarumar gudummawa a yakin da ake yi da talauci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China