Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta bude wurare biyu ga hukumar IAEA
2020-08-27 13:38:23        cri
Gwamnatin kasar Iran da hukumar makamashin nukiliya ta duniya(IAEA) a jiya Laraba sun fitar da wata hadaddiyar sanarwa kan hadin gwiwar da ta shafi batutuwan nukiliya. Sanarwar ta bayyana cewa, Iran ta bude wasu cibiyoyin nukiliyarta biyu bisa radin kanta ga hukumar don taimaka mata wajen gudanar da ayyukan bincike a kasar.

A kwanakin baya ne dai, babban sakataren hukumar IAEA Rafael Grossi ya isa birnin Tehran, inda ya gana tare da yin shawarwari da shugaban kasar Hassan Rouhani da ministan harkokin wajen kasar Mohammad Javad Zarif da kuma shugaban kungiyar kula da harkokin makamashin nukiliyar kasar Ali Akabar Salehi bi da bi.

Sanarwar hadin gwiwa da sassan biyu suka bayar bayan shawarwarin ta ce, an riga an tsai da lokacin da hukumar ta IAEA za ta shiga wadannan wuraren biyu. Kuma hukumar za ta gudanar da bincike bisa ka'idar adalci da rashin nuna bambanci, bisa yarjejeniyar ba da tabbaci daga dukkanin fannoni da takardar karin bayanai da kuma ka'idojin IAEA. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China