Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zarif ya ce Amurka ta yiwa Iran illa ta hanyar takunkumi
2020-03-08 17:09:33        cri
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya zargi Amurka da aikata ta'addanci kan Iran ta hanyar kiwon lafiya.

A sakonsa na twita a ranar Asabar Zarif ya ce, shugaban kasar Amurka Donald Trump yana kokarin tsananta haramtaccen takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar da nufin jefa Iran cikin matsanancin hali game da kayayyakin aiki da kasar ke bukata wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, yayin da jama'ar kasar Iran ke ci gaba da mutuwa.

Ya kara da cewa, "Duniya ba za ta yi shiru ba kan ta'addancin tattalin arzikin da Amurka ke kaddamarwa ta hanyar ta'addancin dake shafar bangaren kiwon lafiya".

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Abbas Mousavi ya sanar a ranar Alhamis cewa, yanayin da Iran ta shiga a sanadiyyar annobar cutar numfashin ta COVID-19, ya nuna a fili irin illolin da takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar ke yiwa rayuwar al'ummar kasar Iran a wannan halin da ake ciki.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da tayin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yiwa kasar na bayar da tallafi wajen yaki da annobar cutar COVID-19, inda ya bayyana tayin a matsayin munafunci da yaudara.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China