2020-05-03 17:16:43 cri |
Ali Shamkhani, sakataren majalisar koli kan al'amurran tsaron Iran ya wallafa a shafin twita na majalisar a yau Lahadi cewa, yarjejeniyar JCPOA zata mutu har abada ta hanyar yin watsi da kudurin kwamitin tsaron MDDr mai lamba 2231 idan haramtaccen takunkumin makaman Iran ya cigaba.
Shamkhani, ya bukaci kasashen Turai masu ruwa da tsaki kan yarjejeniyar su dauki matakai kan yarjejeniyar game da matsin lambar Amurka.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce, Washington tana duba yiwuwar bin dukkan hanyoyin da suka dace na sabunta takunkumin hana Iran cinikin makamai wanda wa'adinsa zai kare nan da watanni shida masu zuwa.
A ranar Asabar gwamnatin Iran ta yi barazanar cewa, muddin aka tsawaita takunkumin makaman Iran, za'a fuskanci mummunan martani daga kasar. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China