Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya jaddada adawar kasar kan bukatun Amurka na "farfado da takunkumin da aka kakabawa Iran"
2020-08-26 14:05:34        cri
Jiya Talata, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya sake jaddada matsayin kasar Sin na adawa da bukatun da kasar Amurka ta gabatar wa kwamitin sulhu na MDD, ta hanzarta sake dawo da takunkumin da aka kakabawa kasar Iran.

Zhang Jun ya ce, kwanan baya, kasar Amurka ta aika wa kwamitin sulhu na MDD wasika, inda ya bukaci kwamitin da ya gaggauta farfado da takunkumin da aka kakabawa kasar Iran. Bukatar da kasar Amurka ta gabatar, ta sabawa doka, kuma dukkanin bangarorin da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran ta shafa, da ma galibin mambobin kwamitin sulhu na MDD suna ganin cewa, kasar Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, a don haka, ba ta da ikon gabatar da wannan bukata. Kana, babu wani shiri na "farfado da takunkumin da aka kakabawa kasar Iran cikin sauri".

Zhang Jun ya kara da cewa, ya kamata kwamitin sulhu na MDD ya mutunta ra'ayoyin gamayyar kasa da kasa, da nacewa wajen kiyaye amana da kwarjinin kwamitin, da aiwatar da ayyukansa na kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa da kasa yadda ya kamata. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa domin warware batun nukiliyar kasar Iran kamar yadda ake fata.

Shugaban kwamitin sulhu na MDD na wannan wata, kana zaunannen wakilin kasar Indonesia dake MDD, Dian Triansyah Djani ya bayyana cewa, mambobin kwamitin sulhu na MDD ba su cimma matsayi daya kan wannan batu ba, kuma shugaban kwamitin ba zai dauki wani mataki bisa bukatun da kasar Amurka ta gabatar masa ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China