Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya ce mai yiwuwa ba zai halarci taron koli kan batun Iran ba
2020-08-16 17:22:06        cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a ranar Asabar cewa, ba zai halarci taron koli kan batun Iran wanda shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya shawarta a ranar Juma'a ba.

A ranar Juma'a ne kwamitin sulhun MDD ya ki amincewa da bukatar dake neman a sake sabunta dokar takunkumin cinikin makamai kan Iran. Daftarin kudirin, wanda Amurka ta gabatar da shi, bai samu kuri'u taran da ake bukata na amincewa da kudirin ba.

Karkashin kudirin dokar kwamitin sulhun MDD mai lamba 2231, wanda ya amince da yarjejeniyar nukiliyar Iran na shekarar 2015, inda aka daddale tsakanin Iran da manyan kasashen duniya shida da suka hada da Birtaniya, Sin, Faransa, Jamus, Rasha da Amurka, takunkumin haramta cinikin makaman da aka kakabawa Iran zai kare ne a ranar 18 ga watan Oktoban 2020.

Amurka ce kadai ta fice daga yarjejeniyar a watan Mayun shekarar 2018.

Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya fada a ranar Juma'a cewa, a halin yanzu Amurka bata cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran, don haka bata da ikon neman bukatar kwamitin sulhun MDD kan batun.

Ministocin harkokin wajen kasashen Birtaniya, Faransa da Jamus sun bayyana a watan Yuni cewa, ba zasu taba goyon bayan duk wani ra'ayin bangare guda ba wanda zai sauya matsayar MDD kan batun takunkumin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China