Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta gargadi Amurka kan yunkurin dakile man da zata kai Venezuela
2020-05-18 13:48:40        cri
Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa yunkurin da Amurka ke yi na kawo cikas ga tankokin tankon man fetur din kasar Iran dake kan hanyarsu zuwa Venezuela al'amari ne mai cike da hadari kuma tsokana ce, tashar talabijin ta Press TV ne ta bada rahoton.

Zarif ya fadi haka cikin wata wasikar da ya aikewa babban sakataren MDD Antonio Guterres a ranar Lahadi.

Yace gwamnatin Amurka ta kuka da kanta kan duk wani mummunan sakamakon da wannan yunkurin zai iya haifarwa.

Ya kara da cewa, Iran a shirye take ta tinkari duk wasu matakai ko barazanar da wannan yunkurin zai haifar.

A ranar Laraba, wasu kafafen yada labaran yammacin duniya suka bada rahoton cewa wata tankar dakon mai ta yi lodin man a tashar ruwan Iran domin kaiwa kasar Venezuela, wanda hakan zai taimakawa kasar ta kudancin Amurka samun saukin tsananin bukatar man da take da shi a kasar.

Sai dai, fadar White House ta sanar a ranar Alhamis cewa Amurka tana tunani game da matakin da zata dauka na martani kan Iran game da jigilar man da zata yi zuwa kasar Venezuela wacce ke fama da rikici.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China