Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta lashi takobin mayar da martani idan Amurka ta keta yankinta na ruwa
2020-04-30 10:41:27        cri
Kasar Iran ta ce za ta mayar da martini mai tsauri idan jiragen ruwan Amurka suka keta yankin ruwan kasar yayin da suke wucewa.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim, ya ruwaito kakakin rundunar sojin Iran, Abolfazl Shekarchi na sukar Amurka bisa abun da ya kira "tayar da hankali" a mashigin tekun Fasha.

Abolfazl Shekarchi, ya kuma yi watsi da barazanar shugaba Trump na baya bayan nan dake da nufin jan hankalin jama'a, gabanin zaben shugaban kasar.

A makon da ya gabata ne, Donald Trump ya ce ya ba rundunar sojin ruwan kasar umarnin harbin jiragen tsaron ruwan Iran dake matsawa jiragen Amurka a mashigin tekun.

A cewar Abolfazl Shekarchi, ya kamata Amurkawa su sani cewa, idan suka yi wani yunkurin da ya keta yankin ruwan kasar ko muradun al'ummarta, to za kasarsa ta mayar da martani fiye da wanda suka gani a baya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China