Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta kaddamar matakan kandagarkin cutar COVID-19
2020-03-06 10:54:56        cri
Iran ta sanar da kaddamar da wani tsari da zai mayar da hankali kan yaki da barkewar cutar COVID-19 a kasar, a jiya Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na kasar IRNA, ya ruwaito ministan lafiya, Saeed Namaki na cewa, shirin da aka yi wa lakabi da "tsarin kasa na yaki da cutar COVID-19", zai hada dukkan cibiyoyin kiwon lafiya na kasar da masu bada gudummawa karkashin inuwar ma'aikatar lafiyar, ta yadda za su kasance a kusa da jama'a. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China