Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a duniya sun wuce miliyan 20
2020-08-13 14:09:42        cri
Jiya Laraba, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fidda rahoto dake nuna cewa, gaba daya, yawan mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a duniya ya wuce miliyan 20, yayin da mutane dubu 730 suka mutu sakamakon cutar. Hukumar ta kara da cewa, duk da cewa, cutar ta kawo mana babbar asara, amma, muna dab da samun nasarar yaki da cutar baki daya.

Kwanan baya, kasashe da dama sun samu sakamako a fannin nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19. A ranar 11 ga wata, ma'aikatar lafiyar kasar Rasha ta yi rajistar allurar rigakafin cutar COVID-19 ta farko, wadda kasar ta kirkiro. Alkaluman kididdiga hukumar WHO sun nuna cewa, ya zuwa ranar 10 ga wata, ana gwajin allurar rigakafin cutar da nau'o'insu da suka kai 28 kan mutane, kuma nau'o'i guda 6 daga cikinsu sun shiga matakin karshe na gwaji, kana, nau'o'i 3 daga cikinsu kirar kasar Sin ne, sai guda daddaya daga kasashen Amurka, da Burtaniya da kuma nau'i daya na hadin gwiwar hukumomin da suka hada da, kamfanin nazarin kwayoyin halittu na kasar Jamus da kamfanin sarrafa magunguna na Pfizer na kasar Amurka da sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China