Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Darektan CDC: Jinkirin gano COVID-19 daga Turai shi ya haifar da barkewar ta a Amurka
2020-07-30 10:20:17        cri

Darektan cibiyar kandagarkin cututtuka masu yaduwa ta Amurka Robert RedField, a karon farko ya amince yayin wata zantawa da kafar yada labarai ta ABC cewa, gwamnatin Trump ta yi jinkiri wajen fahimtar barazanar cutar COVID-19 lokacin da ta barke a Turai, wadda daga bisani ta haddasa barkewar cutar da ma bazuwarta a kasar ta Amurka.

Redfield ya ce, cutar COVID-19 da ta bullo a kasashen Turai, ta shigo cikin Amurka kafin ma kasar ta fahimci matsalar dake tattare da cutar. Sai dai daga lokacin da gwamnatin Amurka ta farga game da barazanar cutar, har ma ta sanya takunkumi hana tafiye-tafiye kan kasashen na Turai, an shafe makonni biyu zuwa uku, mutane 60,000 na shigowa cikin Amurka a ko wace rana daga yankin Turai, wannan na daga cikin babban dalilin barkewar cutar a Amurka.

Bugu da kari, Redfield ya amince yayin hirar cewa, gwamnatin tarayyar Amurka da ma'aikatar lafiyar kasar, sun tabka kura-kurai a matakansu na yaki da wannan annoba, kana sun gaza a kokarinsu na tantance yanayin cutar. Amma, yana fatan za a ga bayan wannan annoba, idan har jama'a suka hada kai, tare da sanya kyallen rufe baki da hanci, wanda ya ce ita ce hanya mafi dacewa a halin da ake ciki ta hana yaduwar cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China