Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Cutar COVID-19 za ta kara yawan yara masu fama da matsalar rama har miliyan 6.7
2020-07-28 10:26:22        cri
Jiya Litinin, asusun tallafawa kananan yara na MDD wato UNICEF ya fidda rahoto cewa, sabo da mummunan tasirin da cutar numfashi ta COVID-19 ta haifarwa tattalin arzikin duniya, a shekarar 2020, akwai yiwuwar, yawan yara masu fama da matsalar rama, wadanda suke kasa da shekaru 5, zai karu zuwa miliyan 6.7, inda yaran za su yi fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki.

Matsalar rama bisa ilmin likitanci, tana nufin raguwar nauyin jiki sabo da cututtuka ko wasu matsalolin da abin ya shafa, inda nauyin yaro bai kai 90% na madaidaicin nauyin da aka kayyade. Kuma matsalar rama za ta haddasa karin matsaloli ga kananan yara, kamar rashin karfi, rashin girma yadda ya kamata, da matsalar da ka iya kaiwa ga mutuwa

Rahoton UNICEF na nuna cewa, a shekarar 2019, kafin barkewar cutar numfashi ta COVID-19, yara kimanin miliyan 47 a duniya suke fama da matsalar rama. A don haka, idan har ba a dauki matakai yadda ya kamata ba, mai yiyuwa ne, adadin zai karu zuwa miliyan 53.7 a bana.

Bincike na nuna cewa, rabin yaran dake fama da wannan matsala suna zaune ne a kudancin Asiya, yayin da 30% suke kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara. Adadin yara masu fama da matsalar rama zai karu da 14.3% a kasashe masu tasowa dake samun kudin shiga kadan da matsakaici, lamarin da zai haddasa rasuwar yara sama da dubu 10 cikin ko wane wata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China