Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban mashawarcin Trump kan harkar tsaro ya kamu da COVID-19
2020-07-28 09:33:58        cri

Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, babban mashawarcin shugaba Trump na Amurka kan harkokin tsaro Robert O'Brien ya kamu da cutar COVID-19. Kafar yada labarai ta Bloomberg, ta ruwaito cewa, tun a makon da ya gabata ne dai, O'Brien ya daina zuwa ofis, bayan da ta ruwaito cewa, wasu manyan jami'ai sun kamu da wannan cuta.

A cewar daya daga cikin wadannan mutane, jami'in ya kamu da cutar ce, bayan halartar wata liyafa da iyalansa suka shirya, ya kuma killace kansa a gida, inda yake ci gaba da tafiyar da harkokin hukumar tsaron kasa galibi ta wayar tarho.

Sai dai har yanzu ba a san sau nawa O'Brien ya yi mu'amala da Trump a baya-bayan nan ba. A 'yan kwanakin nan, fadar White House ta dakatar auna zafin jikin dukkan wadanda ke shiga harabar fadar. Sai dai har yanzu ana yawan gwada wadanda suka yi mu'amala da Trump.

Jami'ar hulda da 'yan jaridu ta fadar White House Kayleigh McEnany, ta bayyana a yayin taron manema labarai a makon da ya gabata cewa, ana yiwa shugaban gwaji akai-akai.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China