Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD ya bayyana muhimmancin samar da kudin shiga na wucin gadi ga marasa galihu yayin da ake yaki da COVID-19
2020-07-27 12:10:17        cri

Wani jami'in MDD ya jaddada muhimmancin gaggauta samar da kudaden shiga na bukatun da suka zama wajibi ga mutanen da suka fi tsananin talauci a duniya yayin da ake yaki da annobar COVID-19 wadda har yanzu take ci gaba da ta'azzara duniya.

Mataimaki ga babban sakataren MDD, kana daraktan tsara manufofi na shirin raya ci gaban kasashen na MDD UNDP, Xu Haoliang, ya ce aiwatar da shirin MDD yana da matukar muhimmanci ga kasashen da wannan annobar ta fi yiwa mummunar illa domin shirin zai taimaka wajen tabbatar da ci gabansu da ceto yanayin zaman lafiyar siyasarsu, da kawar da rashin daidaito da kuma rage karuwar yaduwar annobar ta COVID-19 a kasashen.

Jami'in wanda ya bayyana hakan a zantarwasa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin da yake tsokaci game rahoton shirin mai taken "Samar da muhimmin kudin shiga na wucin gadi: Ba da kariya ga matalauta da marasa galihu a kasashe masu fama da talauci."

Rahotan ya bayar da shawarwari cewa ya kamata a biya muhimman kudaden shiga na wata wata wanda adadinsa ya kai dala biliyan 199, yin hakan shi ne zai tabbatar da kyautatuwar yanayin zaman rayuwar jama'a biliyan 2.7 da ke fama da talauci a kasashe masu tasowa kimanin 132, a yayin da annobar ke kara kamari a fadin duniya.

Xu ya ce, illar da cutar ke haifarwa ta wuce yadda aka yi tsammani, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a duniya ya wuce miliyan 16, kana adadin masu kamuwa da cutar a kowane mako yana zarce miliyan 1.5. Kuma har yanzu babu wasu alamu dake nuna cewa annobar tana sassautowa.

Domin daidaita matsayin tattalin arzikin duniya da kuma kandagarkin tashe tashen hankula a wasu kasashen duniya sakamakon karuwar talauci, tilas ne shugabannin siyasa su yi amfani da hikimominsu wajen samar da muhimman kayayyakin bukatun yau da kullam da suka zama tilas domin samar da makoma mai kyau ga farfadowar tattalin arzikin duniya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China