Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Ya kamata mu raba allurar rigakafin cutar COVID-19 cikin adalci
2020-08-07 13:35:48        cri

Yayin taron manema labarai da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta kira a jiya Alhamis, shugaba mai kula da harkokin gaggawa na hukumar Michael Ryan ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana gwajin allurar rigakafin cutar COVID-19 nau'i 165 a kasashen duniya, kuma an fara gwajin nau'i 26 daga cikinsu a kan mutane, yayin da shigar da nau'i 6 daga cikinsu mataki na karshe, kuma akwai guda 3 daga cikinsu kirar kasar Sin ne.Wannan babbar nasara ce da aka cimma cikin gajeren lokaci.

A mataki na gaba, ya kamata a tabbatar da tsaron amfani da wadannan allura.

A yayin taron, babban sakataren hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, a yayin da ake gaggauta nazarin allurar rigakafi, ya kamata a maida hankali wajen raba allurar cikin adalci, domin samar da allurar rigakafi ga wadanda ba su da kudin sayensu. Amma, ya kamata kasa da kasa su cimma matsaya daya kan batun, ta yadda dukkanin kasashen duniya zasu iya samun allurar rigakafin cutar COVID-19.

Neman mallakar allurar rigakafin cutar COVID-19 bisa ra'ayi na kashin kai, ba shi da amfani, domin ba za a samu farfadowar kasashen duniya baki daya ba, in babu hadin gwiwar kasa da kasa, in ji babban sakataren hukumar WHO. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China