Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO tana sa ran za a yaki da cutar COVID-19 cikin dogon lokaci
2020-08-02 16:01:16        cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce sakamakon lura da yadda annobar COVID-19 ke kara zama barazanar lafiya ta kasa da kasa, akwai bukatar gudanar da aikin yaki da annobar na tsawon lokaci bisa lura da hasashen da ake yi game da kara yaduwar cutar.

Kwamitin aikin gaggawa na yaki da cutar COVID-19 wanda babban daraktan hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya kafa, karkashin tsarin dokokin kiwon lafiya na kasa da kasa IHR, ya gudanar da taron tattaunawa karo na hudu a ranar Juma'a 31 ga watan Yuli, hukumar WHO ta bayyana cikin sanarwa da ta fitar ta intanet a ranar Asabar.

Kwamitin ya amince cewa, har yanzu annobar babbar barazanar lafiya ce ta kasa da kasa, kana ya jaddada muhimmancin yin aiki tukuru a matakan al'ummomin yankuna, da matakin kasa, shiyya, da kuma matakin kasa da kasa.

Kwamitin ayyukan gaggawan ya shawarci hukumar WHO ta ci gaba da zaburar da al'umma a matakai daban daban da kungiyoyin al'umma da abokan hulda na hadin gwiwar yaki da COVID-19 domin ci gaba da daukar matakan yaki da cutar, da kuma taimakawa mambobin kasashe wajen inganta fannin kiwon lafiya, don karfafa aikin bincike, da yin magani ga mutaten da suka harbu da cutar da kuma aikin samar da alluran rigakafin cutar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China