Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda aka raya sana'ar kiwon tsutsar siliki a gundumar Nayong dake lardin Guizhou
2020-08-11 15:38:09        cri

A bara, Luo Yaomei ba ta san yadda ake kiwon tsutsotsi masu samar da siliki ba ko kadan, ta je gundumar Nayong ne kawai domin kula da yaranta. Amma, a halin yanzu, tana dukufa tare da sauran mazaunan gundumar wajen raya sana'ar kiwon tsutsotsi masu samar da siliki, domin samun wadata.

Deng Ruishi ya kafa kamfanin kiwon tsutsotsi masu samar da siliki na Ruihui a gundumar Nayong dake lardin Guizhou, wanda ya samar da guraben ayyukan yi da dama ga mazaunan wurin. A halin yanzu, akwai karin mutanen dake yin wannan aiki cikin himma da kwazo, kamar yadda Luo Yaomei take yi, kuma wasu daga cikinsu, masu fama da talauci ne. Luo Yaomei ta ce, ko wane wata, tana samun albashi da ya kai kimanin kudin Sin Yuan dubu 5, kuma ta koyi fasahohin kiwon tsutsotsi masu samar da siliki da dama.

A kan yi kiwon tsutsotsi masu samar da siliki a wuraren dake kusa da teku a kudancin kasar Sin, yanzu, ana dukufa wajen raya wannan sana'a a yankin dutsen Wumeng na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, domin taimakawa al'ummomin gundumar Nayong, ta yadda za su fita daga talauci, har su samu wadata. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China