![]() |
|
2020-08-10 19:59:31 cri |
Mataimakin darektan ofishin ba da jagoranci ga aikin kawar da talauci na gwamnatin kasar Sin Ou Qingping, ya shaidawa manema labarai a gun taron cewa, ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta riga ta dauki matakin da ya dace, kan wasu mutane da suke cikin kangin talauci, don taimaka musu fita daga wannan mawuyacin hali.
A cewar Ou, yanzu haka an samarwa dukkanin matalauta inshorar jiyya. A hannu guda kuma, cutar COVID-19, da kuma bala'in ambaliyar ruwa, ba za su dakatar da aikin kawar da talauci, da hana samun ci gaba a wannan fanni ba. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China