Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu hotunan fuskokin murmushi da suka burge mu
2020-08-10 15:47:32        cri

Wani yaro ke nan yake yi wa wani dan jarida murmushi a wurin ibadar Tashihungpo ta birnin Shigatse dake jihar Xizang.

Nan garin Payang ne na birnin Shigatse da ke jihar Xizang ta kasar Sin, garin da ya lalace a sakamakon girgizar kasa da ta auku a shekarar 2015 a kasar Nepal. Yanzu yara na wasa a gaban sabbin gidajen da aka gina a garin.

Dan lardin Shanxi, Yang Maolu ya girbe wata kabewa mai nauyin sama da kilogram 200 a yankin Ali na jihar Xizang dake kan tsauni mai tsayin sama da mita 4500.

Dan jihar Xizang, Zhaxi, dake kiwon kaji sama da dubu 10 a garin Lhaze na birnin Shigatse, a ko wace shekara, yana samun ribar sama da yuan miliyan 1.

Wani mai kiwon tumaki a yankin kiwon tumaki na garin Dingri dake birnin Shigatse. Tumakin yankin Xizang, dake rayuwa a tsauni mai tsayi, su kan ci ciyayi na magungunan gargajiyar Sin, shi ya sa, naman tumakin wurin ba su da warin naman rago.

Hoton da wasu masoya suka dauka a kusa da fadar Potala ta birnin Lhasa na jihar Xizang.

Jihar Xizang, wuri ne mai sanyi, kuma babu isassun iskar Oxygen, duk da haka, mutanen jihar suna da kirki, suna kuma karbar baki da hannu bi-biyu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China