Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kimiyya da fasaha na taimaka mana wajen neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba
2020-08-07 16:23:45        cri

Wang Jinqiang ya shahara a duk fadin yankin ciyayi na Ulgai dake jihar Mongoliya ta gida ta kasar Sin, domin shi kwararre ne a fannin kiwon shanu, har ma ya yi tsawon shekaru 16 yana aikin kiwon shanu.

Cikin 'yan shekarun nan, aikin kiwon shanu ya zama wani aiki ne mai sauki, domin ba sai a je wurin kiwon shanu dake waje ba, ana iya gudanar da ayyuka cikin gida, ta hanyar amfani da fasahar tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou. An sa na'urori a kawunan shanu, domin a tabbatar da inda suke, lamarin da ya sa, adadin shanu da Wang yake kiwo ya karu sosai.

Kwamitin kula da harkokin yankin Ulgai ya kawo wannan fasaha ga Wang Jinqiang, sa'an nan, gwamnatin wurin ta zuba masa jari domin taimaka masa yin amfani da fasahar, da kuma samar musu da bayanan da abin ya shafa, ta yadda masu kiwon shanu zasu duba yanayin yankin kiwon dabbobi ta wayar salula, yayin da kara saninsu game da farashin kasuwannin sayar da dabbobi da sauransu.

Jami'i mai kula da dandalin samar da bayanan dabbobi da ciyayi na yankin, Gao Jungang ya bayyana cewa, yanzu ana iya amfani da fasahar tauraron dan Adama wajen samar da labarai masu amfani ga makiyaya, ana iya sanar dasu labarai akan lokaci, da kuma bada taimako gare su wajen kara adadin dabbobin da suke kiwo. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China