Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An canja wata mahakar ma'adinai da ba a amfani da ita a birnin Fuxin zuwa hanyoyin gasar tseren motoci
2020-08-04 15:35:15        cri

A matsayin tsohon birni na aikin hakar kwal, birnin Fuxin na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin, ya taba fuskantar matsalar sauye-sauye. Cikin 'yan shekarun nan, ya dukufa wajen habaka sabbin hanyoyin neman ci gaba bisa ka'idar kare muhalli. Shi ya sa, aka canja wata mahakar ma'adinai da ba a amfani da ita a birnin, zuwa hanyoyin gasar motoci, lamarin da ya sa, birnin ya cimma nasarar yin kwaskwarima, tare da bin ka'idar kare muhalli.

Ma Qiang mai shekaru 33, yana fatan zama dan wasan tsaren mota, yanzu, ya cimma sabon burinsa ta hanyar gasar tsaren motoci da aka gina a birnin Fuxin.

Kuma, birnin Fuxin yana kan gaba game da aikin gyara mahakar ma'adinai zuwa hanyoyin gasar tsaren motoci, wanda ya sa, ya kammala aikin yin kwaskwarimar tattalin arziki, yayin da ya kuma cimma nasarar kyautata muhalli.

Kyautata muhalli tare da neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, ya samar da sabbin damammaki ga birnin Fuxin, ta yadda ya samu babbar bunkasuwa.

A shekarar 2019, gaba daya, an yi gasar tseren motoci sau shida a birnin Fuxin, kuma, mutane sama da dubu dari 2 sun kalli gasar a birnin. Sakamakon haka, birnin Fuxin ya kulla yarjejeniyoyin dake shafar harkokin gasar tseren motoci, da ba da hidima ga wadanda suka sayi motoci, da kuma ba da horaswa da sauransu kimanin dari daya. Dangane da wannan lamari, Ma Qiang ya ce, yanayin harkokin cinikayyarsa yana ci gaba da kyautatuwa, sabo da bunkasuwar birnin Fuxin baki daya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China